Cikakken tarihin wannan makarantar ta AN-NURUL HUDA ONLINE QUR’AN, Da kuma AN-NURUL HUDA ISLAMIC EDUCATION CENTRE

Kudirorin da yasa muka assasa wannan makaranta shine:
domin mu cika burin mu na koyar da yara, manya,maza da mata karatun Alqur’ani mai girma,tare da
haddace shi da sauran Ilmomi na Addinin Musulunci ta hanyar yin amfani da hanyar da za ta inganta
fasahar karatunsu da rubutu na Larabci.
Mun samar da wannan makaranta ne a kudancin Nigeria [kasar yarbawa] saboda dalilai kamar haka:


1-Kamar yadda kowa yasani idan har ana maganar ilimin Addinin Musulunci a Nigeria to sai dai ayi
maganar Arewacin Ngeria, musamman game da Ilimin Alqur’ani mai girma, Karantashi da tajwidinsa.
wannan ne yasa muka kudiri aniyar cewa insha Allahu yanda karatun Addinin Musulunci ya kewaye Ko
ina a Arewacin Nigeria toh zamu bada lokacinmu da jikinmu wajen ganin mun yi iya kokarin mu
domin muga ilimin addinin musulunci ya kewaye ko ina a Kudancin Nigeria Kamar yadda ya kewaye
arewacin Nigeria
Domin Abinda yasa nayi wannan maganar shine,
Lokacin da nazo Kudancin Nigeria a ranar 10/3/1435AH, dai dai da 11/01/2014 a matsayin malamin
makaranta
na zo ne da Niyyar zama na wani dan lokaci da baifi shekara daya ba zuwa biyu,
amma yanda na zo na sami mutanen kudancin Nigeria a matsayi na na wanda bai taɓa zuwa kudanci
ba, na riske su game da sha’anin Addinin Musulunci da karatun Al-kur’ani mai girma, a maganar
gaskiya akwai abin takaici da kuma abin haushi da tausayi ga al’ummar mu.
Saboda yanda suke rayuwar su galibinsu babu ruwansu da neman ilimin addinin musulunci
Sai naji Gaskiya idan na koma Arewa Na bar mutanen da na riska a Cikin wannan Hali ban kyauta ma
Addinin Musulunci da al’umma ta ba. Wannan shine dalilin da yasa muka cigaba da zama a kudancin
Nigeria domin mubaiwa addinin mu na musulunci gudumowar da zamu iya, Allah
kataikemu.Musamman A yankin da Na zauna wato Mutane ne Waɗanda ilimin Addinin Musulunci bai
dame su ba
Domin sai kaga mutumin da yayi shekara da shekaru yana musulmi amma bai iya karanta Suratul
fatihar da zai yi sallah da ita ba kuma bai damu ba, Saboda bai san muhimmancin karatun ba! Acikin Ikon Allah Kokarin da muka fara yi shine; kananan yara masu tasowa sune babban abin da
muka fara tunani, domin sune waɗanda idan aka tsaya musu zasu zama wani abu nan gaba saboda
manyansu abin da yafi damun su shine neman kudi da kai yaran su makarantun boko, saboda sun fi
daukar sa da muhimmanci akan ilimin addini!
Cikin ikon Allah mun fara koyar da yara karatun al-Qurani mai girma. A haka muka fara, kuma mun
samu Nasarori ta yanda wasu Har suka Haddace JUZ’U AMMAH, da JUZ’U TABARAKA karatu mai kyau
da tajwidinsa, Wasu ma ta kai Har sun haddace IZU goma [10 hizb] Acikin dan ƙanƙanin lokaci
Har ta kai ga wasu cikin yaran da muka fara koyarwa an samu wasu da suka wakilci wasu daga cikin
jihohin yarbawa a musabaƙar ƙasa [National Qur’anic competition]
Kamar wanda ya gudana a jihar gombe a shekarar 2018 ɗaya daga cikin ɗaliban da muka fara karatu
da su ya wakilci jihar Ogun,
Da kuma wanda akayi a jihar legas a shekarar 2020 Shima ɗaya daga cikin ɗaliban da muke karatu da
su ya wakilci jihar Oyo.
Da yake inda da muke karatun makarantar boko ce kuma makaranta ce ta kwana wato [bording
school] galibin ɗaliban suna zuwa ne daga jihohi daban daban na yarbawa kamar su: legas, da oyo da
sauransu, wasu kuma a nan jihar Ogun ɗin suke, wasu ma muna kusa da su,
To da yawan ɗaliban idan suka gama makarantar bokon [secondary school] to kuma karatun addinin
da muka fara yi da su ya tsaya kenan, tunda babu kuma inda zasu je su cigaba da karatun.
Daga baya duk wanda muka tuntuɓa daga cikin ɗaliban bayan shekara1 zuwa 2 sai muji bai ƙara
komai ba daga abin da ya koya a wuri mu, to abin yana damu mu sosai sai muka fara tunanin yanda
zamu ƙirƙiri wata makaranta wa ɗaliban a kan yanar gizo wato: [online Qur’an Classes] Mai suna:
AN-NURUL HUDA ONLINE QUR’AN
mun ƙirƙiri wannan makarantar ne ta yanar gizo a shekarar 2018, sannan muka fara karatu da ɗaliban
ta yanar gizo[internet] a ranar 24/1/1442AH dai dai da 12/09/2020 kuma mun samu Ƙarin wasu
ɗalibai waɗanda ma bamu sansu ba,Saboda yanda muke tallata makarantar a kafafen sada zunmunta
[social media] kamar su: facebook da whatsapp, da sauransu.
Daga cikin ɗaliban da Muke karatun da su ta yanar gizo yanzun haka zuwa lokacin da muke wannan
rubutun akwai waɗanda suka haddace suratul Al-Baqarah, Ali-imrãn da Nisa’i
wanda har yanzu wannan makarantar ta yanar gizo tana ci gaba da aiki
Amma daga baya sai muka lura cewa Akwai ɗalibai da yawa waɗanda suke da ƙoƙarin karatun kuma
suke son suyi karatun Amman ba za su iya ba saboda rashin kayan aiki kamar su; n aura mai
kwakwalwa, netwokin da sauransu.
Daga nan sai muka fara tunanin yanda zamu ƙirƙiri makaranta ta islamiyya wanda ɗalibai wadan da
suke kusa, za su iya zuwa su dinga karatu a inda muke.
cikin ikon allah haka mu kayi kuma ɗalibai suka fara zuwa, a haka ɗalibai suka cigaba da zuwa muna
karatun Alkur’ani da sauran littatafan addini Har na tsawon wani lokaci.
To sai yawan adadin ɗaliban ya daɗa ƙaruwa domin duk wanda yaji labarin an samu wata makaranta
da ake koyar da yara karatun alƙur’ani da sauran ilimin addini sai ya kawo yaron shi, da kuma yanda mutane suke jin karatun yaran yana faranta musu rai. Amma Sai masu wajen suka tashe mu a
wanjen, sukace basu so mu cigaba da karatu awajen.
Haƙiƙanin Gaskiya wannan hukuncin da masu gurin suka ɗauka bai muna dadi ba,Har ta kai ga munje
mun sami mai wajen sau 3 akan idan ma mun yi mai wani laifi ne to yayi hakuri ya barmu mu cigaba
da karatun, domin gina wa wadannan yaran rayuwa mai kyau a nan gaba, tun da duk wanda yabai wa
yara ilimin addini ya taimaki al’umma ne bawai yaran kaɗai yataimaka ba.
Amma wannan bawan allah yace babu wani laifi da muka yi kawai dai baya so ne, kuma Bai yarda
mu cigaba da yin karatu a wajen ba.
Haka nan muka haƙura da karatun, tun da wajen ba namu bane.
tun ina jin kunyar abin da zan faɗa wa yaran da iyayensu, daga baya dai na rufe ido na faɗi wa iyayen
yaran ga abin da yake faruwa, har wasu daga cikin iyayen yaran suke fadimin cewa ƙabilanci ne mai
wajen ya nuna mana. daman shi mai wajen bayerabe ne su kuma ɗaliban mafi yawancin su hausawa
ne duk da akwai yarbawa acikin su amma hausawa sunfi yawa, amman mu abinda muke ganin shine
dalilin da yasa mai wajen ya koremu shine: saboda bamu biyan shi wani abu na kuɗi,
Haka muka sallami ɗalibai kowa yakoma gida.
Haka ɗaliban suka ci gaba da zama a gida har na tsawon shekara daya da rabi, basu zuwa makaranta
kuma babu abin da suka ƙara akan abinda suka koya bayan daina zuwansu wajen mu karatu,to Abin
yayi mana ciwo sosai kuma bai mana dadi ba matuka,
Daga nan ne sai muka fara tunanin yanda Zamu ƙirƙiri makaranta ko da haya ne zamu kama domin
musami inda ɗalibai zasu ci gaba da karatun addini,
akwai wani massallacin jumu’ah na kungiyar Jama’atul izalatul Bid’ah Wa iqamatussunnah, wanda na
Hausawa ne a kusa da unguwar da muke.
wanda dan uwa sheick Al-mansur Muhammad, ya ke limanci, sai muka hadu da wasu daga cikin
iyayen ɗaliban muka same shi muka fada masa duk halin da muke ciki game da yaran mu, da kuma
yanda muka fara karatu da kuma nasarorin da muka samu amman bamu da inda zamu tsugunna muyi
karatu, ga kuma ɗalibai muna da su masu yawa. ga kuma yanayin yanda yankin kudanci Nigeria yake
ciki, Na rashin damuwa da neman ilimin addini,
duk da shima yasan halinda mutane suke ciki Awannan yankin Amman muka kara tunatar dashi,
domin shima yana shan gwagwar maya da mutenan yankinsa duk domin cigaban addninin musuluci.
Kuma haduwa da mukayi da dan uwa Imam, sheick Al-Mansur Muhammad ya karamana karfin gwiwa
matuka akan cewa insha allah qudirin da muke dasu na koyar da karatun alkur’ani a kudancin Nigeria
zai cika da izinin allah.
Sai yabamu shawarar cewa tunda ga masallaci mai zai hana mudinga tara yaran agurin muna karatu?
Acikin ikon allah muka sami commiti na wannan masallacin muka fadi musu, suka nuna farin cikinsu
matuka akan wannan babbar cigaba da yazo musu, domin a tarihin wannan yankin na imowo ,ijebu
ode jihar ogun,Hausawa sunfi shekara dari [100 years] da zuwa gurin Amman ba’a taba samun
makarantar islamiyya inda yaran su za suje su koyi karantun Addnin musulunci ba, sai da allah ya
kawo mu muka kafa makarantar Islamiyya a wannan yankin, domin Abinda mutanen yankin sukafi
raja’a akai shine neman Kudi Da ilimin Boko [western Education] Cikin ikon allah, comittin masallacin suka amince muka ci gaba da karatu a ranar 6/11/2021 dai dai
da 1/4/1443AH.
Bayan amincewa da commitin masallacin sukayi, sai muka fara tunanin insha allah zamu mayar da
wannan gurin domin yazama mun kafa makaranta tsayyaya wanda zata tsayu da kafarta, muka fitar
da fom wanda kowane ɗalibi zai cike kafin mukarbe shi a matsayin ɗalibi a makarantar, domin abun
yadinga tafiya a cikin tsari,[ registration form], sannan muka kirkiri dokokin da ka’idoji da kowane
ɗalibi da iyaye zasu amince dasu, duk domin tsarin makarantar yatafi dai dai.
lokacin da muka fara bayar da form sai da muka yima aƙalla ɗalibai saba’in 70 zuwa 75 rijista a rana
daya, to da yake yaran suna da yawa sai muka yi korin daukar wasu yan’uwa aiki a makarantar muna
biyansu albashi a kowane wata saboda su dinga tayamu kula da yaran,tayanda mutum 2 zuwa 3 kadai
baza su iya ba. Saboda yawan daliban
Muhimman darussan da ake karantarwa sun hada da: AL – QUR`ANI,TAUHID, HADITH, FIQHU,
TAUHEED da kuma YAREN LARABCI.
Amma yanzu ƙa lubalen da muke samu shine wannan massallacin da muke karatu da ɗalibai,
masallaci ne wanda yake tsakiyar kasuwa, kuma gurin yayi mana kaɗan kamar yanda zaku gani a
hoto da video na gurin, kuma ɗaliban suna kara yawa akullun, domin kusan kowa ce rana munayiwa
sabbin dalibai rijista a wannan makarantar.
Wannan shine takaitaccen tarihin wannan makarantar ta AN-NURUL HUDA [ AN-NUR INTEGRATED
ISLAMIC SCHOOL].

َّة ُزنُى ُراْل ُه َدي لِل َّد ْع َى
ِة َواْل َم ْر َك ُعلُى ِم اْْل ْسالَ ِمي

Dakuma yanda ta kafu Har zuwa yanzu ana karatu awannan makaranta.

kudirori da muke dasu game da wannan makarantar
kudurorin da manufofi da muke dasu suna da yawa amma ga kadan daga ciki;
1- muna so mu tsara ta dai-dai da zamani,ta yanda daliban makarantar za su samu tsaftataccen ilimin
addinin musulunci dana boko a bai daya.
2, Muna so mu Samar da yara masu halin kirki da nagarta acikin Al`ummar mu domin gobe, a kuma
bisa tsarin musulunci.

 1. Muna so mu inganta ka’idoji karatun Alƙur’an da sauran littafan addnin musulunci a tsakanin al
  ummar musulmi Husawa da yarbawa da sauran ƙabilun da suke a zaune a wannan yankin na kudancin
  Nigeria (ƙasar yarbawa ).
 2. Muna so mu Samar da azuzuwan karatun Alƙur’ani da sauran littattafai na ilimin addinin musulunci
  kyauta ga yara masu karamin karfi a cikin al’umma.
 3. Muna so mu bayar da tallafin karatu kyauta ga ɗaliban da suka kware a fannin ilimi a cikin
  al’umma.
 4. Muna so mu kafa kasuwancin da musulunci ya yarda dashi mai albarka da riba Domin ci gaban
  makarantar ta yanda makarantar ba zata dinga dogaro da abinda ɗalibai suke biya ba kafin tabiya
  malamai da ma aikata hakkinsu.
 5. Muna so mu Samar da ingantaccen karatun Alƙur’ani, darussan larabci da kuma koyar da ilimin
  yammacin duniya (boko) wacce za ta kasance tare da koyarwar Musulunci a cikin al’umma. 8. Muna so muyi anfani da wannan damar mudinga ɗakko malamai daga arewacin Nigeria waɗan da
  sukayi ilimin addini da na zamani, kuma basu da aikin yi domin basu aikin yi su dogara da kansu.
  3- manufar neman taimakonku
  Mu Musulmi mun fi fahimta kuma mun san muhimmancin Musulunci da Alkur’ani da sauran Ilimi.
  Kamar yadda wannan Ilimi yake da kima, wasu yaran suna kan titi, suna yawo babu gaira babu dalili.
  wannan wata dama ce da tasa muka assasa wannan makarantar ta AN-NURUL HUDA ta yanda zamu
  hada yara domin koya musu ilimin addinin musulunci. ta hanyar hada su waje guda, a koya musu
  ilimin addinin Musulunci da ilimin boko da kyawawan halaye da kuma nusar dasu akan suji tsoron
  Allah {s w a} da aiki da hakikanin koyarwar kur’ani da karantarwar manzon Allah {s a w} bisa
  fahimtar magabata na kwarai {salafus saalih}.
  Mun yi imani cewa wanda suka san wane ne Allah, kuma suke bin umarnin addininsa kuma suke jin
  tsoron Allah ba za su taba shiga cikin kowane irin mummunan laifi ba, balle su shiga kungiyoyi na
  ta’addanci musamman irin halin da kasar mu Nigeria take ciki. wannan kyakkyawan yunkuri ne wanda
  muke bukatar goyon bayanku matuka. Muna bukatar mu kasance masu zurfin tunani domin kawo ma
  Addinin Musulunci cigaba, dama al ummar kasarmu da duniya baki ɗaya, maimakon mu shiga cikin
  taron don yin gunaguni game da abubuwan da suke faruwa akasar mu Nigeria. Akwai abubuwa da za
  a yi donmin magance rashin ilimin addnin musulunci a tsakanin al umma, kuma bai kamata a bar shi a
  hannun malamai ba kaɗai, masu kuɗi ma suna da rawar da zasu taka acikin wannan tafiyar ta yaɗa
  addinin musulunci.
  Za mu iya yin haka idan kun taimake mu. Kuma muna da imanin cewa za ku taimake mu kuma shi ya
  sa muke ci gaba da sadar da tunaninmu da buƙatunmu zuwa gare ku.
  Da gudummawar ku za mu iya fitar da wasu daga cikin waɗannan yaran daga kan titi mu karkato su
  zuwa makaranta domin su koyi karatun AL-kur’ani mai girma dakuma sauran ilimin addinin musulunci
  ta yanda zasu ji tsoro kuma su bauta ma allah da ya halicce su.
  4- kalubale damuke fuskanta sune:
  1- Rashin tabbataccen waje, domin kamar yanda nayi bayani a baya masallacin da kungiyar izala
  suka lamince mana muna mu ci gaba da karatu da ɗaliban, a tsakiyar kasuwa yake, ta yanda wani
  lokacin ma hayaniyar kasuwa yana dauke hankalin dalibai a lokacin da muke karatu.
  2- kuma wajen ya yiwa daliban kunci, ba zai iya ɗauke adadinsu ba, balle su mori karatu yadda ya
  kamata a wajen
  3- kuma makarantar muna da buƙatar muyi mata rijista a gwamnatance, ta yanda koda nan gaba
  bazamu samu matsala da gomnati ba.
  5- Abubuwan da muke da buka domin dorewar makarantar sune kamar haka:
  1- muna bukatar tabbataccen wuje na ploti/ fili dan gina makarantar.
  Plot/filin da zai gina mana aƙalla azuzuwa guda takwas(8) tare da ofisoshi guda uku(3) da kuma
  ɗakunan kwana na Malamai, aƙalla guda huɗu (4) da kuma ɗakunan ɗalibai na kwana mai girma guda
  biyu, domin ɗalibai da maza da mata waɗanda zasu dinga zuwa daga jihohi daban daban na kasar
  yarbawa, dama maƙwabtansu, Samun Hakan zasu taimaka wajen gudanar da makarantar a bisa tsari mai kyau da inganci.
  2 – muna bukatar abin da za’a gudanar da makarantar dashi na tsawon shekara daya(1) a ƙalla
  3 – muna bukatar gadaje na kwnanan dalibai, wadan da zamu saka a dakunan dalibai
  4 – muna bukatar kujeru da teburansu waɗanda za’a saka a azuzuwan ɗalibai da ofisoshin malamai.
  5 – muna bukatar Islamic library a makarantar [dakin karatu da ya kunshi littatafai na musulunci].
  6 – muna bukatar rijiyar burtsatse domin samun ruwan sha mai tsafta kuma wadatacce
  Duka wadannan abubuwan da muke bukata munyi kiyasin zasu lashe kuɗin da yakai dala dubu sittin
  $70,000 USD [dala dubu saba’in]
  Dai-dai da [Naira miliyan saba’in da dubu dari tara] ₦70,900,000 NGN
  DOMIN TUNTUBA, ZA’A IYA ZUWA MAKARANTAR DOMIN GANI DA IDO KO A KIRA WADANNAN
  LAMBOBIN:
   Hafizh: Nuruddeen Usman
  Shugaban makarantar AN-NUR INTEGRATED ISLAMIC SCHOOL, Igo oya Imowo,ijebu-ode,ogun
  state,nigeria
  Lambar wayar sa: +2348116406059, +2348023276855,
   Ustaz, Imam: Al-Mansur Muhammad
  Babban Imam na masallacin jumu’ah na, jama’atu izalatil bid’ah wa’iqamatissunah imowo,kara, ijebu￾ode, ogun state,Nigeria.
  Lambarwayarsa: +2348071780740, +2348039691935
  Ko kuma zaku iya neman mu a sauran kafafen sada zumunta kamar su;
  whatsapp +2348116406059 Facebook An-Nurul Huda
  AN-NURUL HUDA QUR’AN ONLINE
  Ga wanda Allah yabaiwa da ikon taimakawa, zai iya taimakawa ta hanyar asusun bank na ajiyar
  makarantar kamar haka:
  ACCOUNT NUMBER: 1225404587
  ACCOUNT NAME: AN-NUR INTEGRATED ISLAMIC SCHOOL
  BANK: ZENITHBANK
  MUNA GODIYA ALLAH YA SA KA MUKU DA ALKHAIRI,SANNAN ALLAH YA BAKU IKON Tallafawa, Amin.